17 Maris 2021 - 13:06
Uganda : An Sake Kama Jagoran ‘Yan Adawa Bobi Wine

A Uganda, an sake kama jagoran ‘yan adawa na kasar, Bobi Wine.

ABNA24 : Bayanai sun ce a jiya Litinin ce dai aka kama Bobi Wine bayan ya bi sahun amsu zanga-zangar lumana.

Jawabin da aka wallafa a shafin offishinsa na twitter na nuna cewa Bobi Wine ya jagoranci ‘yan majalisar da sauran shugabanni don nuna adawa da garkuwa da azabtarwa da kuma kisan magoya bayansa a birnin Kampala.

Mahukuntan Uganda na zargin Wine da yunkurin kawo karshen gwamnatin shugaba Yoweri Museveni ta hanyar zanga-zanga.

342/